rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia
  • Yau ake zama a bainin jama'a game da tsige Shugaban Amurka Trump
  • Wasu 'yan kasar Kamaru sun shiga Otel da Shugaba Paul Biya ke ciki a Paris.

Renon Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An bude taro karo na 25 tsakanin Faransa da Afrika

media
Shugabanni masu halartan taro tsakanin faransa da Afirka © Reuters

Kasar Faransa ta bayyana shirin bunkasa kasuwanci da kasashen nahiyar Afrika, kamar yadda ta battar yayin bude taro karo na 25 tsakaninta da kasashen nahiyar.

Shugaban kasar ta Faransa, Nicolas Sarkozy mai masaukin baki, ya tabbatar da haka a gaban shugabannin nahiyar 38 da shugabannin kungiyoyin ‘yan kasuwa 250 daga nahiyar.

Shugabannin gwamnatocin mulkin sojan kasasashen Guinea Conakry da Janhuriyar Niger suna cikin masu halartan taron.

Kasar Madagascar ba ta cikin wadanda aka gayyata, yayin da kasar Zimbabwe ba ta tura wakilai ba, bayan da Faransa ta fitar da sunan shugaba Robert Mugabe daga cikin masu halarta.

A cikin jawabin bude zaman taro shugaban kasra ta Faransa Sarkozy, ya nuna mahimmancin da nahiyar ta Afrika ta ke da shi.