rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia

Renon Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Afrika ta dace da kujerar Majalisar Dinkin Duniya

media

Shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, yace lokaci yayi da dole a dama da kasashen Afrika, a harkokin siyasar duniya.

Yayin da yake jawabi a taron kasar Faransa da kasashen Africa, shugaba Sarkozy yace, ya dace Africa ta samu gurabe a kwamitin Sulhu, dan tofa albarkacin bakin ta.

Shugaban yace, babu yadda za’a tattauna matsalolin duniya, ba tare da kasancewar wakilan Africa a wurin ba.

Daga nan sai yayi alkawarin wuce gaba, wajen ganin an kawo sauyi a kwamitin Sulhun, da zaran Faransa ta karbi ragamar jagorancin kasashe takwas masu karfin tattalin arzikin masana’antu, wato G-8 da kuma G- 20 a cikin shekara mai zuwa.