Isa ga babban shafi
MDD-EU-Sahel

MDD ta bukaci Tallafin gaggawa domin magance Yunwa a yankin kudu da Sahara

Shugabannin kwamitin Tallafi na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai sun nemi kasashen duniya bayar da tallafin gaggawa, domin shawo kan matsalar yunwa da ke addabar yankin Sahel na yammacin Afrika, inda suka bayyana cewa ana bukatar kudi Dalar Amurka miliyan 725 a bana.

Taswairar yankin kudu da Sahara
Taswairar yankin kudu da Sahara RFI/Latifa Mouaoued
Talla

Shuagabar hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya, Helen Clark tace ana bukatar kimanin EURO miliyon 552, cikin gaggawa don taimaka wa yankin.

Kungiyar tarayyar turai ta bayar da tallafin euro miliyon 30, don samar da cimaka ga yara kanana ‘Yan kasa da shekarau biyu, kimanin Miliyan daya da mata masu juna biyu dubu 500, gami da mata masu shayarwa.

Daraktan hukumar abinci da ayyukan gona ta Majalisar Dinkin Duniya, Jose Graziano da Silva yace lokaci na kurewa, don fari na kara matsowa, amma za’a iya kaucewa haka, in aka dauki mataki cin watanni biyu zuwa uku.

A cewar Mista Siva yankin na da sarkakiya, kuma rashin wadatar abinci zai iya kawo tashe tashen hankula, don haka dole a kaucewa faruwar hakan.

Ana sa ran amfani da kudaden, wajen bayar da tallafi ga kusan mutane miliyan takwas a yankin da ya hada da kasashen Burkina Faso da Chad da Mali da Mauritania da Jamhuriyyar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.