rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Senegal

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana zaben tantance gwani na Shugaban kasar Senegal

media
Macky Sall da Abdoulaye Wade Reuters

Yau Lahadi ake gudanar da zaben tantance gwani na Shugaban kasar Senegal tsakanin Shugaba Abdoulaye wade mai neman tazarce karo na uku, da tsohon PM Macky Sall.


Dukkanin alamu na nuna cewa Shugaba Wade dan shekaru 85 da haihuwa, zai yi ban kwana da madafun iko bayan mulkin shekaru 12, inda Macky Sall dan shekaru 50, ke kan gaba saboda dunkulewar da ‘yan adawa suka yi wajen guda domin kawar da Shugaba Wade daga madafun ikon dake neman makalewa akai. Wade ya yi ikirarin zai samu nasara.

Takarar Shugaba Wade karo na uku, ta janyo suka daga ciki da wajen kasar ta Senegal, wadda ta kasance cikin kwanciyar hankalin siyasa tsakanin kasashen Afrika ta Yamma.