rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mali

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hambararren Shugaban Mali Toure ya shaidawa gidan rediyon Faransa yana cikin Mali

media
Hambararren Shugaban Mali Amadou Toumani Touré Getty Images

Hambararren Shugaban kasar Mali Amadou oumani Toure, da sojoji suka kifar da gwamnatinsa ranar Laraba 21 ga watan na Maris, ya bayyana cewa baya hanun sojojin da suka yi juyin mulki.

Toure ya ce yana Bamako babban birnin kasar, kamar yadda ya tabbatarwa gidan rediyon Faransa, RFI, cikin gajeruwar hira ta waya.
 


Makomar hambararren Shugaba Toure, dan shekaru 63 da haihuwa, ya zama abun damuwa kwanaki shida bayan sojoji karkashin Capt Amadou Sanogo sun kifar da gwamnatin kasar ta Mali.

Jakadan Faransa Christian Rouyer, dake kasar ta Mali, yana cikin wadanda suka tuntubi hambararren Shugaba Toumani Toure ta waya.

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS-CEDEAO, ta dakatar da kasar ta Mali, tare da tura wakilai, domin ganawa, ta hanayar mayar da kasar bisa tafarkin demokaradiya. Sojoji sun ce babu dayansu da zai tsaya takaran zaben da zasu gudanar.