Isa ga babban shafi
Senegal

An janye yajin aikin malaman jami'a na kasar Senegal

Malaman jami’a na kasar Senegal sun janye yajin aiki watanni hudu, domin bada damar shiga tattauanawa da sabuwar gwamnati Macky Sall, da za a rantsar makon gobe, bayan kayar da Shugaba mai garin gado Abdoulaye Wade, yayin zaben ranar Lahadi data gabata.

© Reuters/Joe Penney
Talla

Yau aka sake bude azuzuwa, cikin jami’o’in gwamnati, malaman sun ce matsalolin suna nan, amma anyi haka domin ganin yadda sabuwar gwamnatin Sall zata tunkari halin da ake ciki.

Sall dan shekaru 50, tsohon PM, ya doke Shugaba Wade da gagarumin rinjaye yayin zaben shugaban kasa zagaye na biyu, da ‘yan adawa suka dunkule waje guda, kuma suka smau nasarar kawar da gwamnati mai mulki.

Kasashen dunioya duk sun yaba da yadda aka gudanar da zaben kasar ta Senegal data zama abun koyi tsakanin kasashen Afrika ta Yamma da nahiyar Afrika baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.