rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mauritius

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaban Mauritius ya yi murabus domin Adawa da Fira Minista

media
Shugaban kasar Mauritius Anerood Jugnauth a gefen hagu tare da Fira Ministan kasar Navinchandra Ramgoolam bayan rantsar dasu a Port Louis babban birnin kasar ranar 11 ga watan Mayu shekarar 2011 REUTERS/Ally

Shugaban kasar Mauritius Anerood Jugnauth, ya yi murabus sanadiyar rikici tsakanin shi da Fira Minista Navinchandra Ramgoolam, kuma yace ya yi murabus domin bin sahun ‘Yan adawa. Shugaba Anerood ya shaidawa manema labarai cewa akidun gwamnatin kasar ne bai gamsu da su ba, kuma yace a ranar Assabar ne zai yi ban kwana da shugabancin kasar.


Yanzu haka kuma mataimakin shugaban kasar ne Monique Ohsan Bellepeau, zai karbi kujerar shugabancin kasar wanda Mamban Jam’iyyar Fira Minista ne.

Rikicin ya barke ne tsakanin shugabannin biyu saboda yunkurin hadewar gamayyar Jam’iyyun adawa, kuma akan haka ne Fira ministan ya bukaci Shugaban kasa tabbatar da yunkurin Jam'iyyun al’amarin da yasa shi yin murabus.

Ramgololam ya karbi mukamin Fira Minista ne a shekarar 2010, kuma Jam’iyyarsa ce ke da rinjaye a majalisa.

Sai dai Shugaban kasar Tsohon dan siyasa ne a kasar tun a shekarar 1963 wanda ya kafa Jam’iyyar Gurguzu ta MSM. Mista Jugnauth ya taba zama shugaban adawa a Majalisar kasar tsakanin shekarar 1976 zuwa 1982. Kuma ya taba Rike mukamin Fira Minista tsakanin 1982 zuwa 1995 da 2000 zuwa 2003. Kuma tun a shekarar 2003 ne ya karbi shugabancin kasar amma a shekarar 2013 ne wa’adin mulkinsa zai kawo karshe.

Tun samun ‘Yancin kasar daga turawan Ingila a shekarar 1968, aka girka tsayayyar Demokradiyya a Mauritius, kuma kasar tana samun habakar tattalin arziki fiye da sauran kasashen Afrika