rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia
  • Yau ake zama a bainin jama'a game da tsige Shugaban Amurka Trump
  • Wasu 'yan kasar Kamaru sun shiga Otel da Shugaba Paul Biya ke ciki a Paris.
  • Tashin Bam a Kabul na Afghanistan ya kashe mutane 7
  • Saudiya, Daular Larabawa da Bahrain za su shiga wasannin kwallon kafa tare

Renon Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa ta nemi 'ya 'yanta su gaggauta ficewa daga Mali

media
Sojan Mali, lokacin da suka shiga garin Gao

Kasar Faransa ta bukaci Yan kasar ta dake zama a Mali, da su gaggauta ficewa, ganin yadda 'Yan Tawayen abzinawa ke cigaba da samun nasara a kasar. Wannan sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta bayar, na zuwa ne kwana guda bayan Yan Tawayen abzinawa sun kama garin Timbuktu, daya daga cikin garuruwan dake da matukar tarihi a kasar ta Mali.
Rahotanni sun ce, sojin Gwamnati sun gudu daga sansanin su, lokacin da Yan Tawayen dake rike da muggan makamai suka dumfare su, bayan sun kama garin Gao.
Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta bukaci 'Yan kasar ta kusan 5,000 a fadin kasar na Mali, da su fice ba tare da bata lokaci ba.
Al’amura a Mali na cigaba da tabrbarewa, sakamakon cikar wa’adin kungiyar kasashen Afrika ta Yamma, na ganin sojin da suka hambare gwamnati sun mayar da mulkin farar hula, yayin da a bangare daya, 'Yan Tawayen ke cin karensu babu babbaka.

Maus sharhi kan al’amuran yau da kullum na zargin kungiyar ECOWAS da sakaci wajen rashin daukar mataki kan 'Yan Tawayen, abin da ya kaiga juyin mulki a kasar.