rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

CAF Eritria Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

‘Yan wasan Eritrea 16 sun yi layar zana a Uganda

media
'Yan wasan Eritrea Flimon Tsegay a gefen hagu da kuma Samuel Berhane DR

Hukumar kwallon kafa a yankin gab aci da tsakiyar Afrika ta CECAFA tace wasu ‘yan wasan kwallon kafar kasar Eritrea su 16 sun salwanta a kasar Uganda bayan sun yi wasa da kasar Rwanda. Hukumar tace an fahimce salwantar ‘yan wasan ne bayan sun yi layar zana daga masaukin su a birnin Kamfala.


Rahotanni sun ce wannan ne karo na hudu da ‘yan wasa ke yin layar zana. Kuma ana ganin sun gudu ne saboda tsira daga mulkin danniya da ake yi a kasashensu.

A shekarar 2007, wasu ‘Yan wasan Eritrea 12 sun taba neman mafaka a kasar Kenya haka ma wasu ‘Yan wasa 13 sun taba neman mafaka a Tanzania.

Yanzu dai hukumar kwallon kafa a yankin ta nemi ‘Yan sandan Uganda su saka ido domin gano ‘yan wasan amma kuma har yanzu mahukuntan Eritrea basu ce komi ba game da salwantar su.