Isa ga babban shafi
Eritrea

Gwamnatin Eritrea tace an samu lafawar rikicin da wasu sojoji suka tayar

Gwamnatin kasar Eritrea tace komi ya lafa a birnin Asmara bayan wasu dakarun kasar sun tayar da boren neman ganin an saki Fursinonin siyasa da kuma kawo sauyi a kasar tare da karbe ikon Ma’aikatar yada labarai.

Sugaban kasar Eritrea, Issaias Afeworki
Sugaban kasar Eritrea, Issaias Afeworki Reuters
Talla

“Komi ya lafa a yau kamar yammacin jiya”, inji Yemane Gebremeskel, kakakin fadar shugaban kasa.

Tuni dai Tankunan Sojojin Eritrea suka mamaye ma’aikatar yada labaran kasar a birnin Asmara, don magance boren da wasu sojoji masu tayar da kayar baya 200 suka yi, wadanda suka kwace ginin don neman ganin an saki fursinonin siyasa da kuma kawo sauyi a kasar.

Rahotanni sun ce, ba a ji karar harbi ba, kuma birnin na Asmara na cikin kwanciyar hankali.

Wata Majiya tace Sojojin Eritrea sama da 100 ne suka abkawa Ma’aikatar yada labarai a babban birnin kasar domin ganin an saki Fusunonin Siyasa. Kuma tun lokacin ne aka katse aikin yada labarai a kasar.

Tun lokacin da kasar ta samu ‘Yancin kai a shekarar 1993, Issaias Afeworki, ke shugabancin Eritrea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.