Isa ga babban shafi
Afrika

Cin hanci da rashawa sun yi kamari a Afrika

Yawancin Mutanen Afrika sun yi imanin gwamnatocin kasashensu suna tafiyar hawainiya wajen yaki da matsalar cin hanci da rashawa, a sakamakon wani bincike da aka gudanar a kasashe 34. Sakamakon binciken yace ‘Yan sanda sun fi kowane bangare gurbacewa wajen karbar cin hanci.

Masu Zanga-zangar adawa da janye tallafin Man fetir a Najeriya suna bukatar magance matsalar cin hanci maimakon cire Tallafi
Masu Zanga-zangar adawa da janye tallafin Man fetir a Najeriya suna bukatar magance matsalar cin hanci maimakon cire Tallafi Utomi Ekpei /AFP/Getty Images
Talla

Binciken yace kashi 56 na mutanen Afrika sun ce akwai gazawa a bangaren gwamnati wajen yaki da matsalar Cin Hanci, inda kuma mutum guda cikin uku ke cewa ana tursasa masu bayar da toshiyar baki.

An gudanar da binciken ne a tsakanin mutanen Afrika kimanin 51,000 wanda aka gabatar a kasar Senegal a ranar Laraba.

Sakamakon bincken ya nuna, ‘Yan sanda ne a sahun gaba tsakanin Jami’an gwamnati a kasashe 34.

Kuma alkalumman binciken sun ce ‘Yan sandan Najeriya ne a sahun gaba da kashi 78 sai kashi 69 a kasar Kenya da Saliyo.

Amma a kasashen Namibia da Mauritius da Cape Verde da kuma Botswana, mutane kalilan ne suka ce suna bayar da cin hanci sabanin kasashen Morocco da Guinea da Kenya da Najeriya.

Wani hasashen da asusun bayar da lamuni na duniya ya fitar yace za’a samu ci gaban tattalin arziki da kashi 5.7 a bana a kasashen Afrika da ke kudu da Sahara.

Sai dai kuma hasashen yace akwai bukatar a samar da ci gaba a bangarori da dama domin rage yawan mutanen da ke rayuwa kasa da Dalar Amurka a yankin.

Hukumar samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya tace kusan kashi 24.8 ne ke fama da karancin abinci, kusan mutane Miliyan 223 a yankin kasashen Afrika da ke kudu da Sahara.

Kuma cikin mutane biyar sai mutum guda ya biya cin hanci kafin ya samu damar a diba lafiyar shi a kasashen.

Sakamakon bincike ya yi kira ga kasashen Afrika su dauki matakan gaggawa domin yaki da matsalar cin hanci domin hakan zai taimaka wajen yaki da Talauci da karancin Abinci da kuma ci gaban Dimokuradiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.