Isa ga babban shafi
Masar

Morsi ya nemi a ci gaba da zanga zangar lumana a kasar Masar

Yau Asabar Hambararren shugaban kasar Masar na kungiyar ‘yan uwa musulmi Mohamed Morsi, ya nemi magoya bayan shi su ci gaba da neman canjin cikin tsanaki, ba tare da tashin hankali ba. Morsi ya yi kirane ne lokacin da aka gurfanar da shi a gaban kotu, bisa zargin yunkurin tserewa daga gidan yari da kai wa ‘yan sanda hari.Har yanzu ‘yan kungiyar ta ‘yan uwa musulmi na ci gaba da yin zanga zanga duk mako, duk da dirar mikiyan da jami’an tsaro ke musu, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwa a kalla mutane 1,400 zuwa yanzu.Kotu ta dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar litinin mai zuwa. 

Magoya bayan Morsi na jama'iyyar 'yan uwa Musulmi ta kasar Masar
Magoya bayan Morsi na jama'iyyar 'yan uwa Musulmi ta kasar Masar REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.