Isa ga babban shafi
Guinea Bissau

Mario Vaz ya lashe zaben Guinea-Bissau

Jose Mario Vaz shi ya lashe zabe shugaban kasar Guinea-Bissau da aka gudanar da gagarumin rinjaye, inda ya samu kashi 62 cikin kashi 100 na kuri’un da aka kada. Dan shekaru 57, Jose Mario Vaz, wanda ya taba rike mukamin Ministan kudin kasar, ya lashe zaben ne da kashi 62 na ku’riun da aka kada a zagaye na biyu, inda ya doke abokin hamayyarsa Nuno Gomes Nabiam.

Jose Mario Vaz, Wanda ya lashe zaben shugaban kasa a Guinée-Bissau
Jose Mario Vaz, Wanda ya lashe zaben shugaban kasa a Guinée-Bissau REUTERS/Joe Penney
Talla

Idan har babbar kotun ta tabbatar da sakamakon zaben, Vaz, wanda ke da ‘ya’ya uku, zai kasance zababben shugaba na farko tun bayan da sojin kasar suka yi bore a shekarar 2012.

A zaben da aka gudanar a ranar 13 ga watan Afrilu Vaz da abokin hamayyarsa sun gaza samun yawan kur’riun da ake bukata, lamarin da ya sa aka je zagaye na biyu.

Yanzu babban kalubale da ke fuskantar Vaz shi ne batun sasantawa da dakarun kasar, lamarin da ya ce zai fi mayar da hankali akai, domin a tarihin kasar, babu wani zababben shugaban kasa da ya taba kammala wa’adinshi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.