Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan bindiga sun sace wani Bajamushe a Adamawa

Wasu ‘Yan bindiga a Najeriya sun sace wani Dan kasar Jamus a Jihar Adamawa lokacin da ya ke kokarin barin gidansa zuwa inda ya ke kayarwa a Makaranta. Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ta tabbatar da sace jami’in kuma tace tana kokarin kubutar da shi.

Taswirar Jihar Adamawa a Najeriya
Taswirar Jihar Adamawa a Najeriya www.medianews.net
Talla

Wani shaidun gani da ido ya shaida RFI Hausa cewa maharan su kimanin shida suka zo saman babur da misalin karfe bakwai na safe, sun rufe fuskarsu da bargo a lokacin da suka sace Bajamushen.

Kakakin rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa Usman Abubakar yace al’amarin ya faru ne a garon Gombi da ke nisan Kilomita 100 da Yola.

Zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta fito ta yi ikirarin daukar alhakin sace Bajamushen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.