Isa ga babban shafi
Mozambique

An halatta wa Mata zubar da ciki a Mozambique

Mahukuntan Kasar Mozambique sun sanya hannu kan dokar halatta Zubar da ciki domin ceto rayuwar mata masu ciki da ke fama da matsala. Dokar ta amince mata su zubar da ciki a lokacin da ya ke wata uku, ko kuma idan an sami cikin ne ta hanyar yi wa Mace fyade za a iya zubar da shi a wata hudu.

nydailynews
Talla

Dokar ta amince a zubar da cikin a asibiti mai kwararrun likitoci da gwamnatin ta amince.

Kungiyoyin likitoci a kasar sun yaba da matakin da gwamnatin ta dauka na amincewa da dokar.

Kasar Mozambique dai tana cikin kasashen Afrika da aka fi samun yawan mace-macen mata a wajen haihuwa musamman kananan yara da ke daukar ciki ba ta hanyar aure ba.

Sai dai kungiyoyin addinin Musulunci da Kiristanci a kasar sun la’anci dokar.

Dr Tanko Zakari Likitan Mata a asibitin koyarwa ta Mallam Aminu Kano da ke Kano a Najeriya, ya ce Hukumomin kasar Mozambique sun kalli al’amarin ta fuskar zubar da cikin ba bisa ka’ida ba.

Dr Zakari yace hukumomin kasar ya dace su kalli matsalar ta fuskar lura da al’adun mutanen kasar da addininsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.