Isa ga babban shafi
Faransa-Chadi

Hollande na ganawa da Deby akan batutuwan tsaron Yankin Sahel

Shugaban Faransa Francois Hollande na wata ganawa da shugaban kasar Chadi Idriss Deby, da nufin tattauna harakokin tsaro a yankin Sahel.Yaki da kungiyar Boko Haram da kasar chadi ke jagorantar wasu kasashe da ke makwabtaka da Najeriya na daga cikin muhimmin batun da za’a tattauna yayin tattaunawar.

Shugaban kasar Faransa François Hollande da Shugaba Idriss Deby Itno na Chadi.
Shugaban kasar Faransa François Hollande da Shugaba Idriss Deby Itno na Chadi. ALAIN JOCARD / AFP
Talla

A cikin ‘yan kwanakin baya da shugaba Idris Deby ya ziyarci tarrayar Najeriya, ya koka da rashin musayar bayanai tsakanin dakarun kasashen Nijer, Chadi da Kamaru da na Najeriya kan yakin da sukeyi da Mayakan Boko Haram.

Deby ya ce wannan al’amari ya karya lagwansu, amma ko yanzu da saura, akallar sojojin Chadi dubu 5 ke cikin wannan fada, yayinda 71 ya zuwa yanzu ‘yan Boko haram din suka hallaka yayin fafatawa daban daban.

Wata maganar itace batun dakile safarar makamai a yankin sahel, ko tarwatsa kungiyoyin ta’ada irinsu IS, musaman kasancewar Boko Haram tayi mubaya’a ga kungiyar.

Kasar Chadi na da muhimanci sosai wajen katse lakar kungiyoyin biyu, da ke iya aikewa Juna mayakan da makamai musaman kasancewar IS a kasar libiya da ke iyaka da kasar ta Chadi, duk da cewa dai faransa na da barikin soja a kasar ta Chadi, hada karfi wajen yakar yan ta’ada tsakanin kasashen ya zama wajibi

Banda batun tsaro akwai batun hulda tsakanin Faransa da Chadi da shugaba Hollande da deby za su tattauna yayin wannan haduwa a birnin Paris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.