Isa ga babban shafi
Tunisia

'Yan yawon bude ido na tserewa daga Tunis

An fara kwashe dubban 'yan yawon bude ido daga kasar Tunisia, bayan harin da aka kai Jiya Juma'a a wani wurin shakatawa da ke gabar ruwa. wanda ya hallaka akalla mutane 38, galibinsu Turawa 'yan kasashen yamma.

'Yan yawon bude Ido da ke tserewa daga Tunis
'Yan yawon bude Ido da ke tserewa daga Tunis REUTERS/Zoubeir Souissi
Talla

Rahotanin sun ce Tuni masu yawon bude ido da suka je hutu kasar, suka yi layin shiga jirgi domin barin kasar a filin jirgin saman Hammamet da ke kusa da Tunis.

Tunisia ta ce akasarin wadanda aka kashe a harin 'yan kasar Burtaniya ne lamarin da ya sa Firayi ministan birtaniya David Cameron cewa 'yan kasarsa su shirya domin sun rasa mutane dama.

Mayakan ISIL dai sun dau alhakin kai wannan harin.

Wannan dai ba shi ba ne karon farko da ake kai harin akan 'yan yawon bude ido a Tunisia ba, ko a kwana baya sai da aka kai makamanciyar wannan harin a gidan adana kayan tarihi Bardo da ke kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.