Isa ga babban shafi
Libya

EU ta bayyana amncewa da sabuwar yarjejeniyar zamn lafiya a Libya

Kungiyar kasashen Turai ta yi marhaba da sabon shirin yarjejeniyar zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar wa kasar Libya, a wani mataki na kawo karshen rikicin kasar da ya jefa al’ummah kasar a cikin mummunan hali.

Taron zaman lafiyan Libya da aka yi a Masar
Taron zaman lafiyan Libya da aka yi a Masar REUTERS/Stringer
Talla

Yau shekarar 4 kenan da kasar libya ta fada a cikin tashin hankali tun bayan hambarar da gwamnatin Moamer Kadhafi, tare da kashe tsohon shugaban.

Bayan rabuwar kawunan gwamnatin da aka samu a kasar da ake tafka rikicin ikon tafiyar da mulkin kasar, ayyukan kungiyoyin ta’addanci na kara ta’azara rikicin kasar.

A yanzu dai Yarjejeniyar ya samu goyon bayan ‘Yan majalissun kasar da wasu mambobin jam’iyyun siyasa da kungiyoyin fararan hula.

Majalisar Dinkin Duniya ta dau tsahon watanin wajen kokarin samar da haddin kai tsakanin bangarorin gwamantin kasar 2, domin gudanar da sabon zabe da kafa gwamantin guda

Tuni dai Kungiyar kasashen Turai da kasar Italia suka nuna farin cikinsu da yarjejeniyar, da ake da yakini zata dawo da zaman lafiya a kasar.

Fraiminista kasar Italiya Matteo Renzi, ya ce baya ga samar da zaman lafiya a Libya, yarjejeniya zata taiamaka matuka wajen dakile ayyukan bakin haure dake kwarara Turai ta kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.