Guinea Bissau
Shugaban Guinea Bissau ya rusa gwamnatinsa
Shugaban kasar Guinea Bissau Jose Mario Vaz ya rusa gwamnatinsa a yau Alhamis saboda sabani tsakanin shi da Firiminista Domingos Simoes Pereira. Kafofin yada labaran Gwamnati ne suka bayar da sanarwar rusa gwamnatin.
Wallafawa ranar:
Talla
Sabani tsakanin shugaban kasar da Firaministansa na neman jefa kasar cikin rudanin siyasa inda tun dawo da mulkin dimokuradiya bayan juyin mulkin da Sojoji suka yi a 2012 shugabannin ke rikici da juna.
A watan Yulin 2014 ne aka kafa gwamnatin Pereira bayan Jose Mario Vaz ya lashe zaben shugaban kasa karo na biyu a watan Mayu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu