An saki wasu jami'an tsaro a Darfur
Yan tawayen yankin Darfur na kasar Sudan sun saki wasu jami’an tsaron kasar 18 da suka share tsawon lokaci tsare a hannun su, bayan da kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa Red Cross ta shiga tsakani. Ofishin kungiyar ta Red Cross a yankin na Darfur ya ce an saki sojoji 13, ‘yan sanda uku da kuma fararen hula biyu inda tuni suka isa garin Nyala fadar gwamnatin lardin Kudancin Darfur.
Wallafawa ranar:
A daidai lokacin wanan juma’a ne kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da zama na musamman a game da halin da ciki a Sudan ta Kudu, sakamakon fadan da ake ci gaba da yi tsakanin dakarun gwmanati da na ‘yan tawaye duk da cewa bangarorin biyu sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsu.
Kasar Amurka ce dai ta gabatar da bukatar gudanar da zaman a gaban kwamitin mai kasashen 15, kuma akwai yiyuwar sanya takunkuman kan wadanda ke da hannu a rikicin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu