Isa ga babban shafi
Mali-MDD

An kama mutanen da suka kai hari a birnin Bamakon kasar Mali

Gwamnatin kasar Mali ta bayyana kama wasu mayakan jihadi da ake zargi da kai harin baya bayan nan a Bamako babban birnin kasar, tare da yi barzanar kashe ‘yan jaridun dake yiwa kafofin yada labaran kasashen waje aiki a kasar. 

Wani Bom da aka samu bai tashi ba a kasar Mali
Wani Bom da aka samu bai tashi ba a kasar Mali AFP PHOTO / HABIBOU KOUYATE
Talla

Wata sanarwar da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar, ta nuna cewa dakarun gwamnatin kasar ta Mali ne suka kama mutanen da suka hada da guda 3 da suka shirya kai harin ta’addanci a kan rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Mali wati MINUSMA, a cikin daren Asabar zuwa safiyar Lahadin da suka gabata.

Daukacin mutanen uku yan asalin yankin kudancin kasar ta Mali ne, a yayinda daya daga cikinsu ya kasance dan asalin kasar Cote D’Ivoire, daya kuma dan Burkina faso, dukkaninsu kuma ana zarginsu ne da hannu a cikin harin da aka kai a kan ginin Majalisar Dinkin Duniya dake birnin Bamako, da kuma wata cibiyar ‘yan sandan kasar, da wanda aka kai a kan dakarun tsaron kasar a wajen birnin na Bamako.

Wata majiyar kusa da binciken da ta bukaci a sakaya sunanta, ta sanar da kamfanin dillancin labrun Faransa na AFP Cewa, daukacin mutanen 5 sun amsa laifin da ake tuhumarsu da aikatawa.

Kasar Mali dai na ci gaba da jin jiki, daga hare haren da mayakan Islama, da kuma na ‘yan tawayen Abzinwa da ake ta kokarin ganin an cimma yarjejeniyar zaman lafiya mai dorewa dasu, a taron neman zaman lafiyar kasar, dake yi a Algeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.