rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Syria UNESCO Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kayyayakin tarihin Syria na gab da karewa Muddun aka yi sakaci.

media
Baalshamin a Palmyra Photo : Wikipedia

Hukumar Kula da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ta yi Allah wadai da tarwatsa daya daga cikin tsoffin wuraren tarihi dake Palmyra na kasar Syria sakamakon hare haren mayakan kungiyar ISIL,Hukumar tace ya dace a dauki matakan gaggawa don hana Kungiyar  karas da kayyayakin tarihin kasar


Kungiyar ISIL mai da’awar kafa daular Islama a Gabas Tsakiya ta tarwatsa wasu muhimman kayayyakin tarihi a Palmyra dake da dogon tarihi a cikin kasar a jiya lahadi.

Dama can kungiyar, ta sha kaddamar da hare hare kan muhimman gine gine na kayan tarihi a wasu kasashen Gabas ta Tsakiya,

Darektan kula da kayayyakin tarihi na Syria Mu’amun Abdulkarim, ya yi gargadin cewa sannu a hankali, cibiyoyin tarihi da hukumar kula da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana, suna dab da zama tarihi idan ba’a kula ba.

Tuni dai kungiyar ta ISIL, ta ragargaza mutum mutumin Baal Shaamin da wani wajen ibada na Bel mai shekaru sama da dubu biyu.

Kungiyar kula da muhimman wuraren tarihi ta Syria ta bayyana cewa ya zuwa yanzu, irin wadannan hare hare, sun yi sanadiyar lalata cibiyoyi fiye da 900 a shekaru 4 da ake gwabza yaki a kasar.