rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kogi Najeriya Zaben Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Matsayin INEC kan makomar APC a zaben Kogi

media
Dan takarar Gwamnan Jihar Kogi a Jam'iyyar APC Prince Abubakar Audu wanda ya rasu a ranar Lahadi bayan kammala zaben gwamnan Kogi a ranar Assabar naijanewsmag

Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce tana jiran Jam’iyyar APC ta sanar da ita a hukumance game da rasuwar dan takararta na gwamna a zaben Jihar Kogi Prince Abubakar Audu wanda ya rasu kafin a kammala zaben.


A hirarsa da RFI Hausa, Kakakin Hukumar Nick Dazang ya ce har yanzu suna sauraren APC akan rasuwar Prince Audu.

Mista Dazang ya ce sai idan APC ta sanar da su sannan za su diba dokokin zabe da tanadin da kundin tsarin mulki suka tanadar kan idan haka ta faru.

Kakakin Hukumar INEC Nick Dazang 23/11/2015 - Daga Bashir Ibrahim Idris Saurare

“ Za mu yi amfani da kundin tsarin mulki da dokokin zabe domin tabbatar da adalci”, a cewar Nick Dazang.

Dan takarar gwamnan na APC Prince Abubakar Audu ya rasu ne bayan hukumar zabe tace ba a kammala zaben Jihar Kogi ba da aka gudanar a ranar Assabar.