Isa ga babban shafi
Tunisia

Shekaru 5 da kaddamar da zanga-zangar Larabawa a Tunisia

A yau Alhamis Kasar Tunisia ke cika shekaru 5 da kaddamar da juyin juya halin kasashen Larabawa wanda ya yi sanadin kawar da shugaba Zine El Abidine ben Ali daga karagar mulki, sannan zanga-zangar ta bazu zuwa kasashen larabawa da dama.

Zine el-Abidine Ben Ali na Tunisia  da Hosni Moubarak na Masar
Zine el-Abidine Ben Ali na Tunisia da Hosni Moubarak na Masar © Reuters
Talla

Matasa ne suka jagoranci zanga-zangar da ta kauda shugabannin Yankin dan neman sauyi kan yadda ake shugabancin kasashensu.

Baya ga Zinul Abidine na Tunisia, Zangar-zangar ta yi awon gaba da Shugaban Masar Hosni Mubarak da ya shafe shekaru 30 saman mulki da Kanal Ghaddafi na Libya da shugaban Yemen Abdallah Saleh.

Yanzu kuma ana gwabza fada a Syria domin kawar da gwamnatin Bashar al Assad.

Zababben shugaban Tunisia na Farko Beji Caid Essebsi zai gabatar da jawabi ga ‘Yan kasar a yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.