Gwanki akalla 1,200 aka kashe a Afrika ta Kudu
Gwanki akalla 1,200 aka kashe cikin shekarar data gabata a kasar Afrika ta Kudu, abinda ke nufin farautar gwankin ya karu fiye da yadda yake a baya, duk da cewa ya ragu bisa al’kaluman da aka fitar na shekarar 2014, masana dai sun ci gaba da yiwa mafarauta gargadin kaucewa farautar dabbar don gushewar ta daga doron kasa
Wallafawa ranar:
Masana na cewa yawaitan farautar Gwanki da kashe su babu izini na biyo bayan yawaitan bukatar kahon da ake samu daga kasashe kamar su China da Vietnam.Inda suka yiwa mafarautar dabbar gargadin dakatar da dabi'ar kashe Gwankin don hana gushewar ta daga doron kasa.
Ana dai ci gaba da tafka mahawara akan bukatar halasta cinikin kahon gwanki ko ah ah
Garin da ake samu bayan sarrafa kahon dai, ana anfani da shi ne a matsayin maganin cutar Sankara ko cancer dama wasu cututuka dake addabar dan’adam.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu