SYRIA
MDD ta ce ranar juma'a za a ci gaba da taron sulhunta rikicin Syria
Majalisar Dinkin Duniya ta ce taron sulhunta bangarori masu hamayya da juna a rikicin Syria wanda ya kamata a fara a yau litinin, an amince cewa sai a ranar juma’a mai zuwa ne za a buda shi, inda za a ci gaba da tattaunawa har na tsawon watanni 6.
Wallafawa ranar:
Talla
Manzon Majalisar na musamman a Syriya Steffan de Mistura, ya ce yanzu haka ana kokarin warware sabani dangane da wadanda za su wakilci ‘yan adawa zuwa wannan taro da zai gudana a birnin Geneva.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu