Dubban mutane sun fice yankin Darfur na Sudan
Majalisar Dinkin Duniya sama da mutane dubu dari da Talatin da hudu suka fice yankin Darfur na kasar Sudan saboda gwabza fada ake yi tsakanin dakarun Gwamnati da ‘Yan tawaye.
Wallafawa ranar:
Jami’ar hukumar jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya tace mutanen sun fice saboda fada da ake yi tsakanin Sojojin Gwamnati da ‘Yan tawaye a yankin Jebel Marra mai tsaunika.
Yankin Jebel Marra dai ya dade karkashin ikon ‘Yan tawayen SLA da suka jima suna fada da gwamnati tun a 2003.
Majalisar Dinkin Duniya tace fararen hula kimanin 19,000 suka fice Jihar arewacin Darfur yayin da 15,000 suka tsere daga Jihar tsakiyar Darfur.
Kuma yawancin wadanda suka tsere wa rikicin Mata ne da yara kanana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu