Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

EAC ta karbi Sudan ta Kudu a matsayin mamba

Kungiyar kasashen da ke yankin gabashin Afrika EAC ta karbi sabuwar kasar Sudan ta kudu a matsayin daya daga cikin wakilan kungiyar wadda ta ke bunkasa dangantaka da kuma kasuwanci.

Shugaban kasar Soudan ta Kudu Salva Kiir a birnin Addis Ababa na Habasha
Shugaban kasar Soudan ta Kudu Salva Kiir a birnin Addis Ababa na Habasha REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Yanzu haka kungiyar da ke da cibiya a birnin Arusha na kasar Tanzania na da wakilan da suka hada da Burundi da Kenya da Rwanda da Tanzania da Uganda.

Shugaban kungiyar kuma shugaban kasar Tanzania John Magufuli ya ce yanzu haka mutanen da ke kasashen da ke da wakilci a kungiyar sun kai miliyan 150.

Sudan ta Kudu wadda ta sami 'yancin kai a shekarar 2011 daga Sudan, ta fada cikin rikice-rikice, al’amarin da ya kai ga rasa rayukan dubban mutane tare da tilasta wa miliyoyi tserewa daga gidajensu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.