Isa ga babban shafi
Sahel

Kasashen G5 Sahel zasu kafa rundunar tunkarar ta'addanci

Kasashen 5 da ke Yankin Sahel sun amince su kafa wata rundunar agajin gaggawa wadda zata dinga kai dauki kan masu yiwa Yankin barazana musamman daga kungiyar Al Qaeda da mayakan ISIS.

Shugabanni Kasashen G5 Sahel
Shugabanni Kasashen G5 Sahel AFP PHOTO / IBRAHIM ADJI
Talla

Ministocin tsaron kasashen da suka fito daga Yankin ne suka sanar da haka bayan wani taro da suka yi a kasar Chadi dan ganin sun samar da tsaro a Yankin da sannu a hankali ke zama sansanin Yan ta’adda.

Mai magana da yawun Kasashen na Nijar, Chadi, Burkina Faso, Mali da Mauritania da ake kira kasashen G5 Sahel Najim Elhadj Muhammed ya ce zasu girke sojoji 100 kowanne daga cikin su wadanda aka yiwa horo na musamman dan karkade yan ta’addan.

Faransa da kungiyar kasashen Turai sun bayyana shirin taimakawa kasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.