rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Senegal Fasaha Kimiya Ilimi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Masana kimiya na taro a Senegal

media
Shugaban Rwanda Paul Kagamé tare da Shugaban Senegal Macky Sall a taron masana kimiya da Next Einstein ta shirya SEYLLOU / AFP

Masana kimiya daga nahiyar Afirka tare da masu fada aji da kuma matasa na gudanar da wani taro a kasar Senegal da niyyar hana kwararru daga nahiyar ficewa zuwa nahiyar Turai tare da ganin gwamnatocin Afirka sun fadada aikin bincike kan kiyon lafiya da lissafi.


Masu shirya taron na kasar Senegal na fatar ganin sun sauya yadda kwararru daga Afirka ke tsallakawa zuwa Turai don gudanar da bincike da kuma samun albashi mai tsoka.

Kungiyar da ta shirya taron da ake kira Next Einstein Forum ta yi misali da wani taro kan nazarin cutar Ebola da aka yi a Amurka inda babu masani guda daga Afirka ko kuma ma’aikacin kiwon lafiya daga Afirka ta Yamma da aka gayyata.

Thierry Zomahoun, Daraktan Cibiyar koyar da kimiyar lissafi ta Afirka yace injiniyoyi ‘yan Afirka da ke aiki a Amurka, sun zarce wadanda ake da su a Afirka.

Ana sa ran taron na kwanaki uku da ya gayyato mahalarta daga kasashe 100 na duniya zai yi bayani kan yadda wani salon lissafi zai kai ga samar da rigakafin cutar Zika da kuma yadda wani kididdiga zai nuna yadda makarantu ke gazawa wajen bai wa dalibai ilimin da ya dace.