Isa ga babban shafi
Ebola

Ebola ta dawo a Liberia

Cutar Ebola ta sake dawowa a kasar Liberia bayan mutuwar wata mata da ta harbu da annobar cutar a jiya alhamis kamar yadda hukumomin kiwon lafiya a kasar suka tabbatar.

Cutar Ebola ta dawo a Saliyo da Guinea bayan tabbatar da kawar da cutar baki daya
Cutar Ebola ta dawo a Saliyo da Guinea bayan tabbatar da kawar da cutar baki daya KENZO TRIBOUILLARD / AFP
Talla

A makonnin da suka gabata kasar Liberia kamar dai sauran kasashen yammacin Afkrka da suka yi fama da cutar sun bayyana kawo karshenta, abin da kuma hukumar lafiya ta duniya ta tabbatar, sai dai kwanaki kadan bayan sanarwar, an sake samun wadanda suka kamu da annobar a Guinea da kuma wannan karo a Liberia.

An sake samun bullar cutar ne a Monrovia fadar gwamnatin kasar, kuma wata mata ce yar kimanin shekaru 30 a mutu sakamakon kamuwa da cutar.

Yanzu haka hukumar lafiya ta duniya WHO sun tafi yankin da cutar ta sake bulla a Monrovia domin daukar mataki.

Ebola dai ta kashe Kimanin mutane 4,800 a Liberia kafin sanar da kawar da cutar a kasar a watan Disemba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.