rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zaben Nijar Nijar Mahamadou Issoufou

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An rantsar da Issoufou na Nijar

media
Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou. atlasinfo

A yau Asabar aka rantsar da shugaban Nijar Mahamadou Issoufou a wa’adin shugabanci na biyu bayan ya lashe zaben kasar zagaye na biyu da aka gudanar a ranar 20 ga watan Maris mai cike da kalubale.


An gudanar da bikin rantsar da shugaban ne dai a birnin Yamai fadar gwamnatin Nijar a gaban shugabannin kasashen Afrika kimanin 9 da suka halarci bikin.

Issoufou ya rantse da al Qaur’ani mai tsarki bayan ya samu nasara da kashi 92.51 na kuri’a a zaben da ‘yan adawa suka kaurace.

A cikin jawabin shugaban bayan rantsar da shi ya jaddadda cewa zai mayar da hankali wajen yaki da ta’addanci tare da kokarin magance wasu matsalolin ‘yan Nijar.