rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Djibouti Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mata 'Yan Kasar Djibouti 9 na Yajin Cin Abinci Saboda Sojan Faransa Sun yi Masu Fyade

media
Shugaban kasar Djibouti Ismail Omar Guelleh a wani taro a Addis-Abeba. REUTERS/Tiksa Negeri

Wasu mata tara ‘yan kasar Djibouti dake gudun hijira a Faransa sun shiga rana ta 13 suna yajin kin cin abinci saboda zargin laifukan fyade da sojan Faransa ke yiwa mata dake kasar su.


Matan sun ki cin abinci sai dai kawai ruwa, da shayi suke ta sha tun lokacin da suka fara yajin kin cin abinci.

Mata ‘yan kasar Djibouti 10 suka shiga wannan yajin kin cin abinci a Paris amma daya daga cikin su ta jingine yajin ranar Juma’a data gabata.

Matan na kwance ne a bisa kananan gado da suna baza a wani yanki dake kudancin Paris.

Hudu daga cikin matan sun bayyana cewa sojan Faransa sun yi masu fyade a lokacin da suka tafi kasar su aiki.