rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Cutar Lassa Katsina Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Lassa: Mutum guda ya mutu a Katsina

media
Lassa ta sake fara bulla a Taraba a Najeriya wikimedia

Hukumomin Jihar Katsina a Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutun guda da ya kamu da cutar zazzabin Lassa a Jihar, yayin da wani kuma ke kwance a asibiti, tare da kuma sanya ido kan wasu mutane 100.


Kwamishiniyar lafiya Maryam Bala Usman ce ta tabbatar da bullar cutar a Jihar Katsina.

Sannan tace suna tsare da mutum guda mai shekaru 27 da bincike ya tabbatar da yana dauke da cutar Lassa.

Hajiya Maryam ta ce suna jiran sakamakon gwajin jinin da aka yi wa mutumin da ya rasu domin tabbatar da ko cutar Lassa ce ta yi sanadin rasuwar shi.

Ana dai kamuwa da cutar Lassa ne daga abincin da Bera ya gurbata da gubar bakin shi ko mu’amula da wadanda ke dauke da cutar.

Sama da mutane 200 hukumar lafiya a Najeriya ta tabbatar da cewa suna dauke cutar a jihohin kasar kusan 20. Sannan Cutar ta kashe mutane kusan 100.