rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Zaben Nijar Diflomasiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kafa Majalisar Ministoci a Jamhuriyar Nijar

media
Mahamadou Issoufou Shugaban kasar Nijar atlasinfo

An kafa sabuwar majalisar ministoci mai mambobi 38 a jamhuriayr Nijar, kwanaki 10 bayan rantsar da Issoufou Mahamadou akan wa’adin mulkin kasar karo biyu.


Sabuwar majalisar ministocin wadda aka sanar da kafawa a cikin daren jiya, ta kumshi tsoffi da kuma sabbin fuskoki a cikinta, domin 15 daga cikin tsoffin ministoci da suka taba yi aiki da gwmanatin da ta gabata sun dawo a cikin gwamnatin.

Dukkan jam’iyyun da ke da wakilci a majalisar dokokin kasar sun samu mukamai a wannan sabuwar gwamnati, yayin da aka damka sauran mukaman a hannun wadanda suka dafawa Shugaba Issoufou domin samun nasara a zaben shugabancin kasar zagaye na biyu.

Tsohon ministan harkokin wajen kasar Bazoum Mohamed ne aka nada a matsayin ministan cikin gida, yayin da aka mika ragamar ma’aikatar tsaron kasar a hannun Hassoumi Massaoudou wanda shi ne ministan cikin gida a gwamnatin da ta gabata.

Tsohon mataimakin daraktan mulki a fadar shugaban kasar, wanda kuma ya tsaya takarar a zaben shugabancin kasar Ibrahim Yacouba ne aka bai wa mukamin ministan harkokin waje.

Wasu daga cikin sabbin fuskoki a gwamnatin sun hada da Kassoum Moctar tsohon magajin garin Maradi da aka bai wa ma’aikatar gidaje, sai Lawan Magaji a matsayin ministan ayyukan jinkai, yayin da ministan albarkatun mai Foumakoye Gado da takwaransa na ma’aikatar kudi Seidou Sidibe suka ci gaba da rike mukamansu.