An sake kawar da Ebola a Guinea
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO tace an kawo karshen barkewar cutar Ebolar da aka sake samu a kasar Guinea, amma hukumar ta yi gargadi akan cutar na iya sake bulla.
Wallafawa ranar:
Wakilin hukumar Aboubacar Gaye ya ce an sallami mutumin da ya kamu da cutar na karshe a watan Afrilu kuma yanzu haka an kwashe kwanaki 42 ba tare da samun wani ya kamu da cutar ba.
Sakoba Keita, jami’in yaki da cutar a Guinea ya ce mutane 3,814 aka tabbatar sun kamu da cutar yayin da kimanin 2,544 suka mutu.
Cutar dai ta sake bulla a kasashen Guinea da Liberia da Saliyo bayan ta yi kisan dubban mutane a kasashen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu