Isa ga babban shafi
Algeria

Mutane 33 sun mutu a hatsarin mota a Algeria

Anyi wani mummunar hatsarin mota a kasar Algeria, jiya asabar inda mutane 33 nan take suka mutu.  

Taswirar kasar Algeria
Taswirar kasar Algeria CIA
Talla

Hukumomin kasar sun bayyana cewa akwai kuma mutane 22 da suka jikkata sakamakon karo gaba-da -gaba tsakanin wata mota Bus shake da fasinja da kuma wata katuwar motar dakon kaya.

Mutanen da suka jikkata an kwashe su zuwa asibiti ana yi masu jinya.

Alkalumma na nuna a duk shekara mutane 4,000 suke rasa rayukansu a hadduran motoci a kasar Algeria.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.