rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Habasha Eritria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Eritrea na takun-saka da Habasha

media
Shugaban Eritrea Isaias Afwerki madote.com

Hukumomin Eritrea sun zargi Habasha da kai hari kan sansanin sojinta da ke kan iyaka da kasashen biyu ke rikici da juna.


Ma’aikatar yada labaran Eritrea ta ce dakarun Habasha sun kai harin ne a Yankin Tsorona, sai dai mai Magana da ywun gwamnatin Habasha Getachew Redda ya ce ba su da labarin wata taho mu gama da aka yi.

Eritrea ta samu ‘yancin kai daga Habasha a shekarar 1991 bayan sun shafe shekaru suna yaki da juna.

Kuma ko bayan samun ‘Yancin kan Eritrea, sun sake gwabza yakin shekaru biyu tsakanin shekarar 1998 zuwa shekara ta 2000.

Kasashen dai na rikici ne kan garin Badme da ya yi iyaka da kasashen biyu wanda Majalisar Dinkin Duniya ta ba Eritrea amma har yanzu yana karkashin ikon Habasha.