rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Habasha Eritria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ban Ki-moon ya shawarci Habasha da Eritrea su kai zuciya nesa

media
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ©REUTERS/Heinz-Peter Bader

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya bukaci kasashen Habasha da Eritrea da su kai zuciya nesa domin kawo karshen hare haren da ake samu akan iyakokinsu.


Mai Magana da yawun Sakataren, Stephaine Dujjaric yace Ban ya bayyana haka ne lokacin da ya gana da Firaminsitan Habasha Hailemariam Desalegn a Brussels, yayin da mataimakin Sakatare Janar Jan Eliasson kuma ya tattauna da ministan harkokin wajen Eritrea ta waya.

Ban ya bukaci kasashen biyu su warware sabanin su ta hanyar tattaunawa maimakon daukar makamai.

Kasashen dai na rikici ne kan garin Badme da ya yi iyaka da kasashen biyu wanda Majalisar Dinkin Duniya ta ba Eritrea amma har yanzu yana karkashin ikon Habasha.