rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Honduras Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Honduras Ta Kama Bakin Haure 109 Daga Kasashen Afrika

media
Shugaba Juan Orlando Hernández na kasar Honduras Reuters

Gwamnatin kasar Honduras sun karas da cewa su na tsare da wasu bakin haure 109 daga kasashen Africa da ke kokarin tsallakawa zuwa yankin Tsakiyar Amurka don tafiya cikin kasar Amurka.


Wani Jami’in Hukumar kula da shige da fice na kasar ya bayyanawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa suna duba yiwuwar barin mutanen  su tafi ko kuma a tsare su.

Mai Magana da yawun Hukumar kula da shige da ficen ya bayyana cewa mutanen sun hada da manya 100, da kananan yara tara da suka fito daga kasashen Janhuriyar Democradiyya ta Congo, Mali, Senegal da Burkina Faso kuma an kama su ne suna tattaki da kafa akan iyakan Honduras da kuma Nicaragua.

Jami’in mai suna Rene Vindel ya fadi cewa za’a gudanar da bincike domin tantancewa ko masu aikata laifuka ne, sannan a barsu amma kuma ba za’a bari su wuce kwanaki uku ba.