wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa
Eritrea ta ce Habasha na shirin afka mata da yaki

Gwamnatin kasar Eritrea ta shaidawa Majalisar Dunkin Duniya, MDD cewa makwabciyar ta Habasha na take-taken fara yaki gadan-gadan tsakanin su.
Wani mashawarcin shugaban kasar Eritrea, Yemane Ghebreab ya shaidawa komitin Kare Hakki Bil'adama na MDD cewa yanzu haka Habasha na ta shirin fara yakin ne.
Yemane Ghebreab na gaban kotin ne domin kare zargin da ake yiwa kasar tasa cewa tana shirin sojan ta domin fara yaki.
Kasashen biyu na ta zargin juna da takalan fada a kan iyakokin su.