Uganda tana kwashe ‘Yan kasarta daga Sudan ta kudu
Manyan motoci da tankokin yakin Sojin Uganda sun kutsa kai Sudan ta kudu domin fara kwashe fararran hula da suka makale a birnin Juba, a yayin da ake furgabar yiyuwar sake ballewar rikici a jaririyar kasar.
Wallafawa ranar:
Rikicin dai ya lafa sakamakon tsagaita wuta tsakanin dakarun gwamnatin shugaba Salva Kiir da na Mataimakin shi Riek Machar.
Bangarorin biyu sun shafe kwanaki biyar suna barin wuta a Juba babban birnin Sudan ta kudu. Amma Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin sake barkewar wani sabon rikici.
Shugaba Salva Kiir a yau Alhamis ya bukaci Sulhu da mataimakinsa Riek Machar.
Kiir ya yi wa Machar tayin tattaunawa domin tabbatar da zaman lafiya a kasar, inda ya bukaci kawo karshen zubar da jini a Sudan ta Kudu.
A safiyar alhamis din nan ne tawagar motocin sojin Uganda 50 dauke da manyan makamai suka shiga kasar domin taimakawa fararan hula da ke gudun hijira daga Juba.
Babban hafsan sojin Uganda Brigadier Leopold Kyanda ya ce tawagar na dauke da soji dubu biyu wadanda za su shafe tsawon kwananki biyu zuwa uku a Juba domin kwaso mutanen kasar saboda barazanar barkewar yaki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu