Isa ga babban shafi
Najeriya

Sarkin Musulmi ya la’anci kisan da aka yi wa Lazarus Agai a Filato

Sarkin al’ummar Musulmin Najeriya Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar na uku ya yi allawadai da kisan gillar da aka yi wa daya daga cikin manyan Sarakunan Jihar Plateau, Saf Ron Kulere Lazarus Agai.

Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar tare da Gbong Gwom na  Jos
Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar tare da Gbong Gwom na Jos facebook
Talla

Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara fadar shugaban Sarakunan Jihar Filato Gbong Gwom Jos, inda ya bukaci kai zuciya nesa da barin jami’an tsaro su yi aikin su wajen gano wadanda suka aikata Kisan.

Sultan Abubakar ya bayyana cewar kisan gillar na zuwa ne a dai dai lokacin da mutane a ciki da wajen Jihar Filato ke yabawa da zaman lafiyar da aka samu a Jihar.

Sai ya yi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta zakulo wadanda suka kashe Basaraken domin ganin an hukuntasu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.