Isa ga babban shafi
Malawi

'Yan sanda Malawi sun cafke mutumin da ya sadu da 'yan mata 100

A kasar Malawi, ‘Yansanda sun kama mutumin nan da ke dauke da kwayar cutar HIV kuma ya sadu da ‘yan mata sama da 100 da sunnan al’adar, bayan an biya shi kudi.

Eric Aniva da ake kira da  “Kura” a kauyen Malawi, Iyayye na biyansa kudi domin saduwa da 'yan mata
Eric Aniva da ake kira da “Kura” a kauyen Malawi, Iyayye na biyansa kudi domin saduwa da 'yan mata
Talla

An gurfanar da Mutumin mai suna Eric Aniva a gaban kotu bisa laifin cin zarafin yara kanana da kuma zargin yada cutar HIV a kasar.

Mista Aniva da ya sadu da ‘yan mata sama da 100, ya ce ya yi hakan ne bisa umarnin iyayen ‘yan matan dake biyansa kudi, don saduwa dasu da sunan al’adar tsarkake ‘ya’yan nasu kamar yadda yake a al’adar al’ummar yankin kudancin kasar ta Malawi

Shugaban kasar Malawi Peter Mutharika ne dai ya bayar da umarnin kama Mista Aniva bayan kafaffen yada labaran kasar sun dauki labarin yadda ake biyanshi kwatakwacin dalar Amurka hudu ko bakwai don yin Jima’I da kowacce mace guda, shugaba Mutharika ya bukaci gudanar da bincike ga rawar da iyalan ‘yan matan suka taka tare da tantance lafiyarsu

Gwamnatin Malawi ta dadde tana adawa da wannan al’ada inda yanzu haka ta bukaci wargazata baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.