An yi shafin Facebook na Hausa
Shafin zumunta na Facebook ya kirkiro da shafin Hausa, sakamakon yadda hausawa ke amfani da shafin kamar sauran kabilu a duniya. Facebook ya kaddamar da tsarin ne a 1 ga watan Agusta 2016.
Wallafawa ranar:
Yanzu Hausa ta samu shiga sahun harsunan Afrika a Facebook bayan harshen Somalia da Swahili da Afrikaans da Kinawarwanda.
Hausa harshe ne da mafi yawancin mutanen kasashen yammacin Afrika ke amfani da shi musamman a kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Ghana da Benin.
Kusan mutane miliyan 40 ke amfani da harshen Hausa a duniya.
Akwai shafukan Facebook a harsuna sama da 100.
Idan mutum na son komawa Facebook Hausa zai je Settings sai ya sauya harshe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu