Isa ga babban shafi
Burundi

Burundi ta yi watsi da batun turamata 'yansanda

Hukumomin kasar Burundi sun yi watsi da shirin aikewa da ‘yan sanda 228 zuwa kasar, kamar dai yadda wani kuduri na MDD ya amince a yi.

Wasu 'yan kasar Burundi dake zanga zanga a Bujumbura
Wasu 'yan kasar Burundi dake zanga zanga a Bujumbura STR / AFP
Talla

Gwamanatin Burundi ta ce ba a tuntube ba kafin daukar wannan mataki, saboda haka ba za ta amince da shigar dakarun zuwa cikin kasar ba.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya ya amince da a tura jam’an tsaro zuwa Burundin a kokarin ganin an kawo karshen rikicin da kasar ke fama da shi sama da shekara daya.

Kwamitin tsaron ya cimma matsayar cewa jami’an ‘yansandan da za'a tura zasu shafe tawon shekara guda a kasar ta Burundi.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.