Isa ga babban shafi
Afrika

ANC na fuskantar barazana a zaben Afrika ta Kudu

Sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar a Afrika ta kudu zai bayyana matsayin jam’iyyar ANC da ta share fiye da shekaru 22 tana shugabancin kasar. A yau ne ake saran fitar da sakamakon wanda zai nuna ko dai jam’iyyar ta rasa tagomashinta a idon al’ummar kasar ko kuma a’a.

Yau ake saran fitar da sakamakon zaben kananan hukumomi a Afrika ta Kudu yayin da jam'iyyar ANc mai mulki ke fuskantar barazana rashin samun nasara
Yau ake saran fitar da sakamakon zaben kananan hukumomi a Afrika ta Kudu yayin da jam'iyyar ANc mai mulki ke fuskantar barazana rashin samun nasara RAJESH JANTILAL / AFP
Talla

Tun bayan da aka rantsar da Nelson Mandela a matsayin shugaban kasa a shekara ta 1994, jam’iyyar ta ANC ke samun fiye da kashi 60 cikin 100 a dukkanin zabukan da ake gudanarwa a Afrika ta Kudu.

Sai dai a wannan karon ana tantama game da samun nasararta.

Matsalar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta da cin hanci da rashawa da kuma rashin ayyukan yi, duk sun haifar da nakasu ga martabar jam’iyyar a yanzu.

Miliyoyin al’ummar kasar ne suka fito don kada kuiri’a a jiya Laraba, inda ake ganin sun yi azamar ganin bayan jam'iyyar ta ANC.

Rahotanni sun ce, babbar jam’iyyar adawa ta Democratic Alliance da ke rike da Cape Town, ta yi wa takwararta ta ANC zarra a babban birnin Pretoria.

Sai dai wata kuri’ar jin ra'ayin jama’a da aka gudanar a farkon wannan makon ta nuna cewa, akwai karamar nasara da jam'iyyar ANC din ka iya samu a zaben kananan hukumomin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.