Isa ga babban shafi
RFI

Har yanzu ba shaidu a shari’ar Wikilin RFI Hausa a Kamaru

Bayan sake zaman shari’ar wakilin RFI Ahmed Abba a wata kotun Yaounde a Kamaru, har yanzu an kasa gabatar da shaidun da ke tabbatar da zargin da ake ma Dan jaridar na alakar shi da kungiyar Boko Haram.

Wakilin RFI Hausa Ahmed Abba a Marwa wanda Kamaru ke ci gaba tsarewa
Wakilin RFI Hausa Ahmed Abba a Marwa wanda Kamaru ke ci gaba tsarewa facebook
Talla

An yi zaman shari’ar ne a ranar Laraba kuma lauyan da ke kare dan Jaridar Maitre Charles Tchoungoug ya ce har zuwa wannan lokaci kundin tuhumar ba ya kunshe da wani laifi akan Abba bayan share tsawon watanni shida ana shari’ar.

Lauyan ya ce kundin na kunshe ne kawai da Bahasin Malam Abba kuma ba ya kunshe da wani laifi.

Ahmed Abba dai na aiko wa RFI Hausa rahotanni ne daga Marwa arewacin Kamaru kuma ya share tsawon shekara daya a tsare bayan kama shi a ranar 30 ga watan Yulin 2015 ba tare da an same shi da aikata wani laifi ba.

Hukumar gudanarwa ta kafafen yada labaran Faransa da ke watsa shirye-shirye zuwa kasashen ketare, ta bayyana damuwarta a game da ci gaba da tsare Abba, musamnan lura da yadda aka azabtar da shi tsawon watanni uku a birnin Youande.

Hukumar RFI na ci gaba da kira da babbar murya ga mahukuntan Kamaru su saki Dan jaridar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.