Isa ga babban shafi
WHO

An kaddamar da rigakafin Shawara a Congo da Angola

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da wani gagarumin aikin rigakafin cutar zazzabin Shawara a kasashen Congo da Angola dan dakile yaduwar cutar da kuma hana ta yaduwar ta zuwa kasashen duniya.

Zazzabin shawara ya samo asaline daga Angola
Zazzabin shawara ya samo asaline daga Angola Scott Olson/Getty Images/AFP
Talla

Heather Kerr, Daraktan kungiyar Agaji ta Save the Children ta shaidawa RFI cewa, mutane miliyan 14 za a yiwa rigakafin.

Kerr, ta ce matsalar na da matukar girma, kuma ta samo assali ne daga kasar Angola, kuma tsakanin Congo da Angola yau an samu mutane 947 da suka kamu da cutar, wadda tuni mutane 451 sun mutu.

Jami’ar ta kuma bayyana yadda aka samu wadanda suka fitar da cutar daga Afirka, cikin su harda wasu ma’aikata ‘yan kasar China da suka koma gida daga Angola.

Kana cutar ya yadu zuwa Turai da Arewacin Amurka, saboda haka akwai fargabar cewar masu dauke da cutar na iya yada ta a cewar, Kerr.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.