Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram: Kerry ya yaba wa Sojin Najeriya

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya jinjina ga Najeriya a game da irin nasarar da kasar ke samu akn mayakan Boko Haram. Amma ya yi gargadi Sojojin akan yadda suke wuce gona da iri wajen yaki da ta’addanci.

Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry
Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry REUTERS
Talla

Kerry wanda ke zantawa da manema labarai a birnin Sokoto da ke arewacin Najeriya, ya ce dole ne a jinjina wa jami’an tsaron kasar, sakamakon kwace muhimman yankuna da kuma ‘yanto dubban mutane daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram.

A cewar shi Sojojin Najeriya sun ‘yanto dubban fararen hula, sannan daruruwan ‘yan Boko Haram ne suka yi saranda, tare da kama kwamandojin kungiyar da dama.

A cikin makon da ya gabata sojojin na Najeirya sun kaddamar da mummunan farmaki wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mayakan Boko Haram masu tarin yawa.

Kerry ya ce Sakamakon taimakon da ta ke samu daga dakarun rundunar hadin-gwiwa na kasashen Amurka, Faransa da kuma Birtaniya, a yau Najeriya ta samu gagarumar nasara wajen rage karfin kungiyar Boko Haram

Sannan ya ce kasashen Kamaru da Nijar da Chadi da kuma Benin, sun taka gagaruwar rawa domin tabbatar da tsaro akan iyakokin Najeriya.

Amma Mista Kerry ya yi gargadi ga Sojojin tare da jaddada girman kare hakkin Dan Adam.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama dai sun zargi Sojojin Najeriya da wuce gona da iri wajen kisan fararen hula da sunan farautar ‘Yan Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.